Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Jarida Ya sha Duka a Jihar Bauchi


Makiraho
Makiraho

Kamar yadda bincike ya nuna shi dai wannan dan jaridar ya na gabatar da shirin siyasa ne a lokacin da mutanen su uku suka dirkaki gidan radiyon suka fada masa da duka.

A jihar Bauchi wani dan jarida mai suna Ibrahim Bababah dake aiki a gidan radiyon Albarka FM mai zaman kanta, mallakar tsohon Babban daraktan gidan radiyon tarayyar Najeriya kuma tsohon ma’aikacin gidan radiyon muryar Amurka Mallam Ladan Salihu, ya sha duka a lokacin da wasu magoya bayan wata jam’iyyar siyasa suka yi dirar mikiya a gidan radiyon.

Dan jaridar ya ce a lokacin da ya ke gabatar da turmi na biyu na shirin siyasar da ya ke gabatarwa ne wadannan mutane suka shigo dakin da ake gabatar da shirye shirye suka haushi da duka.

Shugaban ‘yan jarida na jihar Bauchi Mallam Ibrahim Malam Goje ya ce kungiyar ta yi zaman gaggawa don nazarin yadda za a bi diddigin batun, kuma ta yi Allah wadai da abun da ya faru.

Ga wakilinmu a Bauchi Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG