Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bikin Al'ada A Kasar Habasha Ya Haddasa Mutuwar Mutane Fiye da Maitan


Gawarwakin wasu da suka mutu cikin turmutsitsin da ya faru biyo bayan harba harmen barkonon tsohuwa da 'yansanda suka yi
Gawarwakin wasu da suka mutu cikin turmutsitsin da ya faru biyo bayan harba harmen barkonon tsohuwa da 'yansanda suka yi

Wani buki na al’ada da aka saba gudanarwa kowace shekara a kasar Ethiopia ya haddasa mutuwar mutane masu yawa jiya lahadi, a lokacin da ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa tare da yin harbi da harsasai a sama don kashedi ga masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.

Wannan mummunan lamari ya faru a garin Bishoftu, kimanin kilomita 40 a kudu maso gabas da Addis Ababa, babban birnin kasar.

Shaidun gani da ido sun fadawa VOA cewa wadanda suke halartar wannan buki da ake kira IRREECHA sun harzuka a lokacin da wani basaraken gargajiya na kabilar Oromo mai suna Abba Gadaa, yake jawabi, suka kuma nuna adawarsu da daga tutar gwamnatin Ethiopia a kusa da Dandalin da yake wannan jawabi.

Wasu matasa sun kutsa kan Dandalin suka yi kokarin tuge wannan tutar, inda jami’an tsaro suka rufe su da duka. ‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa, sai mutane suka firgita suka sheka da gudu. Da yawa daga cikin wadanda suke gudun sun fada cikin wasu ramuka masu zurfi da aka haka a kusa da inda ake gudanar da bukin.

Wasu da suka jikata a tattakin
Wasu da suka jikata a tattakin

Jami’an yankin sun ce mutane 52 sun mutu. Amma shiadu a wurin sun fadawa VOA cewa mutane akalla 100 suka rasa rayukansu.

Ana zaman tankiya sosai a tsakanin al’ummar kabilar Oromo da gwamnatin tarayya ta Ethiopia a cikin shekara gudan da ta shige. ‘Yan kabilar ta Oromo sun fusata sosai a watan Nuwambar bara, a bayan wani shirin da gwamnati ta yi na fadada bakin iyakar babban birnin kasar, abinda zai shiga cikin gonakinsu da kuma yankunan dake karkashin ikon gwamnatin lardin Oromo.

XS
SM
MD
LG