A karo na hudu tun makon jiya bama-bamai suke tashi a birnin Maiduguri fadar jihar Borno, tun bayan kama aikin sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.Wanda ahalin yanzu yake rangadi a kasashen Nijar da da Cadi dangane da fitinar da bindigar suke haddasawa kasashen hudu, Najeriya, Nijar, da Cadi da Kamaru.
Wannan karon, bam din ya tashi ne a kofar shiga wani gareji dake unguwar da ake kira Baga Road, a yammacin jiya laraba.
Mazauna unguwar sun gayawa wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biu cewa, suna kyautata zaton an ajiye bam din ne a kofar shiga garejin.
Shaidun gani da ido suka ce mutane akalla bakwai ne suka halaka. Wani daga cikin wadanda suka yi magana da wakilinmu yace makwabcinsa yana daga cikin wadanda fashewar ta jikkata.
Har zuwa yanzu dai babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wadannan hare hare, ciki har da wanda aka kai a kasuwar dabbobi ko mayanka ranar talata. Amma suna kamada irin aika-aikar 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.
Ga karin bayani.