Dan wasan Barcelona dan kasar Ajantina Lionel Messi, ya sake kafa tarihin a fagen tamola a wasan da Barcelona ta lallasa takwararta Espanyol da kwallaye 4-0 a gasar Laliga mako na 15 a bana.
Dan wasan ya ci kwallaye biyu daga bugun tazara (free Kick) hakan ya taimakawa Barcelonana cigaba da zama akan teburin Laliga da tazarar maki uku a saman Sevilla mai maki 28.
Karon farko kenan da Messi ya ci kwallaye biyu a wasa daya daga bugun tazara a tarihin rayuwarsa a kulob din bangaren gasar La Liga na kasar Spain.
Dan wasan Messi ya ci kwallayen ne daga gefe daban-daban, kwallo ta farko a gefen dama, ta biyu kuma daga gefen hagu ana mintuna 65, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Messi ya ce zai yi kokarin ci gaba da zurara kwallaye daga bugun tazara (Free Kick).
Dan wasan na Argentina yana da yawan kwallaye 17 a dukkanin wasannin da ya buga wa Barcelona tare da taimakawa aka jefa guda Goma a bana.
Wannan nasarar ta Barcelona ya nuna cewar ta shirya wa haduwar da za tayi da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a gasar zakarun Turai matakin rukuni a ranar talata mai zuwa, sai dai tuni Barcelona ta haye zuwa zagayen gaba inda take matsayi na daya da maki 13.
Ita kuwaTottenham tana mataki na biyu a rukunin da maki 7 dai dai da Inter Milan wacce take mataki na uku, za'a buga wasanne a Camp Nou, da zaran Tottenham ta samu nasara a wasan zata tsallaka zagayen gaba.
Facebook Forum