Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wane irin Shiri Afrika Ta Yi Wa Coronavirus?


Wani ma'aikacin lafiya a Addis Ababa, Ethiopia, ranar 20 ga watan Maris, 2020.
Wani ma'aikacin lafiya a Addis Ababa, Ethiopia, ranar 20 ga watan Maris, 2020.

Afirka, ita ce nahiyar da ke da karancin masu fama da cutar coronavirus, domin daruruwan mutane ne suke dauke da ita idan aka duba jimullar mutum 200,000 da cutar ta harba a duniya.

Sai dai kwararru a fannin lafiya, na ganin cutar za ta iya yin mummunan tasiri a nahiyar wacce tuni fannin kiwon lafiyanta ke cikin wani mawuyacin hali.

Sannu a hankali, cutar coronavirus na yaduwa a sassan nahiyar inda take harbin daruruwan mutane a akalla kasashe 30 da suka hada da Burkina Faso, Kamaru, Ethiopia, Najeriya, Senegal da kuma Afirka ta Kudu.

Mafi aksarin wadanda suka kamu da cutar a kasashen da ke yankin yamma da Sahara ne.

Gargadin Tedros Ghebereyesus Ga Nahiyarsa

Duk da cewa Afirka ce nahiyar da ke da karancin masu dauke da cutar a duniya, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, bai yi wata-wata ba wajen bayyana irin illar da cutar za ta iya yi a nahiyarsa muddin ba a dauki matakan da suka dace ba.

“Ya kamata mu dauki duk matakan da suka dace domin dakile wannan cuta, mu kuma kwan da shirin cewa, cutar za ta iya yin ta’adi, saboda mun ga yadda take yaduwa a sauran nahiyoyi ko kasashe. Saboda haka, ya kamata Afirka – nahiyata, ta mike tsaye.” Shugaban WHO Tedros Adhanom Gebhereyesus ya ce.

Fargabar da jami’an lafiya ke nunawa ita ce, yadda nahiyar take fama da wasu cututtuka a sassanta.

“Har yanzu ba mu san yadda wannan cuta za ta yi tasiri a tsakanin al’umomin da ba su da cikakkiyar kariya ba, misali, a tsakanin al’umomin da ke da masu cutar HIV, ko yaran da ba sa samun abinci mai gina jiki. Abin da ya kamata mu shiryawa kenan.” In ji Dr Maria Van Kerkhove, Kwararriya a fannin lafiya.

Afirka ta Kudu

Mutum 150 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a Afirka ta Kudu – dalilin da ya sa Shugaba Cyril Ramaphosa, ya ayyana tsauraran matakan rage yaduwar cutar.

Hukumomi a kasar sun hana matafiya daga kasashen da cutar ta yi kamari shiga kasar tare da rufe makarantu da kuma haramta tarukan jama’a da yawansu ya haura 100.

Afirka ta Kudu, ita ta fi kowacce kasa yawan masu fama da cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

“Ina ga babu takamaiman bayani kan yadda wannan cuta ke tasiri akan masu cutar HIV, amma idan muka yi la’akkari da yadda sauran cututtukan da ke shafar numfashi suke tasiri akansu, musamman wadanda ba sa shan magani, akwai yiwuwar su fuskanci tsananin rashin lafiya.” In ji Prof. Cheryl Cohen

Wani abu mara dadi da kwararru suka fito karara suka bayyana shi ne, dole sai Afirka ta zauna cikin shiri, domin babu haufi, za a fuskanci mawuyacin hali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG