Dan wasan kungiyar kwallon kafa na Juventus Cristiano Ronaldo, mai shekaru 33 da haihuwa, dan kasar Pirtugal ya bayyana fatansa na ganin
watarana takwaransa abokin hamayyansa Lionel Messi ya canja ra’ayinsa, na karkare kwallon kafarsa a kasar Spain don ya gwada wani bangare a duniya daban, wanda ta hakan ne za a kara gane kwazonshi.
'Yan wasan Ronaldo da Messi dai sun shafe tsawon shekaru 10, suna lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa ta duniya (Ballon d’Or), inda har yanzu suke matsayin ‘yan wasa biyu da babu kamarsu a duniyar kwallo wanda suka kafa tarihinsu.
Ronaldon wanda ya koma kulob din Juventus na kasar Itali daga Real Madrid, kan zunzurutun kudi har yuro miliyan £99 a farkon wannan kakan 2018/19, bayan tsawon zama da yayi a Real har shekaru 9, ya ce dan wasa ba'a gane kwazonsa, sai ya gwada sa’arsa a wasu kungiyoyi daban-daban kafin asan kwazon sosai.
Kafun Ronaldon ya dawo Juventus, ya fara wasansa daga gida Putugal a kungiyar Sporting Lisbon, daga bisani ya koma Ingila inda ya fafata a Manchester United, sai kasar Spain a kungiyar Real Madrid, ya ce ya fuskanci kalubale kafin ya iya canza sheka.
Ronaldo yace ya na fatan abokin nasa Messi zai karbi wannan shawarinsa, kan sauya sheka zuwa daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafar Italiya kamar yadda shima yayi.
Amma idan har yana jindadinsa a Barcelonar kamar yadda ya ke yi a baya, to yana masa fatan alheri, Messi dai bai taba canza sheka zuwa wata kungiya ba tun da ya fara buga wasa a Barcelona sama da shekaru goma.
Facebook Forum