Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Za A Tuntuba Idan An Ga Jinjirin Watan Ramadan


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar

Sarkin Musulmi Abubakar ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.

Majalisar Koli ta Musulunci a Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci Musulmi a fadin kasar da su fara duban jinjirin watan Ramadan na 2025 (1446 AH) daga ranar Juma’a.

Abubakar ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.

“Sakamakon shawarar da Kwamitin Duban Wata na Kasa (NMSC) ya bayar, Shugaban Majalisa yana kira ga al’ummar Musulmi a Najeriya da su fara duban jinjirin watan Ramadan 1446 AH da zarar rana ta fadi a ranar Juma’a, 28 ga Fabrairu, 2025, wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban, 1446 AH.”

Majalisar ta yi addu’a cewa Allah ya ba wa kowane Musulmi rai da lafiya don halartar ibadar Ramadan tare da cin gajiyar albarkar da ke cikin watan.

Majalisar ta kuma bayyana cewa, baya ga shugabannin addini na yankuna da aka saba tuntuba a kowace unguwa, za a iya tuntubar wasu mambobin Kwamitin Duban Wata na Kasa (NMSC) domin tabbatar da sahihin bayani kan ganin jinjirin watan Ramadan 1446 AH.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG