Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fitar da wani jerin Sunayen masu horar da ‘yan wasa watau (Coaches ) wadanda zasu fafata wajan neman zama gwarzon mai horar da ‘yan wasan kwallon kafa na duniya na shekarar 2016, wanda zai gudana ranar 9/1/2017 a Zurich.
Zinedine Zidane na Real Madrid wanda ya samu nasarar cin kofin La-liga na Spain a 2015/2016, Sai Claudio Ranieri na Leicester City da ya lashe kofin firimiya na kasar Ingila na shekarar 2015/2016.
A cikin jerin sunayen akwai Pep Guardiola wanda ya rike Kungiyar Bayern Munich dake jamus wanda a yanzu haka yake rike da Manchester City, ta Ingila tare da Diego Someone na kungiyar Atletico Madrid, da Luis Enrique mai horar da kungiyar Barcelona.
Sunayen sun hada da Jurgen klopp na Liverpool da Mauricio Pochettino na Tottenham dake kasar Ingila tare da mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal Fernando Santos, wanda ya samu nasarar cin kofin zakarun nahiyar kasashen turai wanda ya gudana a Faransa a bana.Har ila yau akwai Didier Deschamps na kasar Faransa, da yazo na biyu a gasar nahiyar kasashen turai da akayi 2016 daga karshe sai Chris Coleman Mai horar da Kungiyar kwallon kafa ta kasar Wales, wanda ya samu nasarar zuwa wasan kusa da na karshe (same final ) a gasar ta kasashen turai.
A ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 2016 za'a karkare fitar da sunayen yan takarar da zasu gwabza a zaben
Kungiyar ‘yan jarida da masu horar da ;yan wasan kwallon kafa tare da kaftin kaftin na kasashe hada da ma'abuta kwallon kafa masu hurda da yanan gizo su zasu jefa kuri'ar domim samun gwarzon a Tsakani.