Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain, wanda ya taka leda a kulob din Barcelona, David Villa, ya bayyana cewar zai ajiye takalman wasansa a wata mai zuwa, bayan da ya shafe shekaru 19 ya na murza tamalo.
Dan wasan wanda ya lashe kofin duniya a shekarar 2010, tare da tawagar kasar Spain kafin nan tun a shekarar 2008, da shi aka lashe kofin nahiyar Turai.
Villa mai shekaru 37, da haihuwa ya samu nasarar daukar kofin Laliga na kasar Spain guda biyu, tare da kungiyar Barcelona daga bisani ya barta.
A wannan shekarar dan wasan ya buga wasa a kulob din Vissel Kobe, kafin zuwan sa ya fafata wasa a kungiyar kwallon kafa ta New York City dake nan kasar Amurka.
David Villa, yace ya ajiye takalman wasansa ne bisa ra'ayin kansa, batare da shawartan kowa ba, haka ba yana nufin ya bar hidimar kwallo bane, zai cigaba da bada gudumawarsa.
A tarihin wasansa ga kasarsa ta Spain ya samu nasarar zurara kwallaye guda 59.
Facebook Forum