Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta nuna a ranar daya ta wannan shekarar an haifi yara kimanin 20,210 a Najeriya.
A cewar hukumar wannan ya nuna yadda ake samun karuwar jama'a cikin sauri a kasar. Ya kamata hakan ya karfafa daukan matakan tazarar haihuwa.
Ana kiyasin nan da zuwa shekarar 2050, Najeriya ce za ta zama ta uku a jerin kasashen da suka fi yawan jama'a a duniya.
Amma hukumar UNICEF ta nuna juyayin cewa wasu daga cikin yaran su na mutuwa tun ranar da aka haife su a saboda matsalolin da ana iya kauce musu.
Kwararre kan kula da lafiyar yara a matakin farko a kasashe masu tasowa Dr. Alagbo ya ce hukumomi na daukan karin matakai. Ya ce an fahimci cewa mata da yara kusan miliyan daya ne ke rasuwa a shekara don haka aka fito da wani tsari da jihohi zasu yi anfani dashi domin a ceto mata da yara daga mace mace. Hukumar ta duniya ta dauki kasashe biyar da suka hada da Najeriya domin a ga tasirin da shirin zai yi. Tsarin zai hana yara mutuwa daga zazzabin cizon sauro da amai da gudawa da ciwon hakarkari.
Ita ko daraktan rigakafi ta hukumar kiwon lafiya a matakin farko Dr Rukaya Wamako ta ce shayar da yara nonon uwa shi ne rigakafin muddin uwa ta na cin abinci ingantace..
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum