Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya yace ana girke sojojin kiyaye zaman lafiya dake Sudan a wasu muhiman wurare kan iyakar arewaci da kudancin kasar, gabannin kuri’ar da kudancin kasar zata kada na neman ballewa.
Shugaban ofishin Majalisar a Sudan, Halie Menkerios, ya fada litinin cewa an tura Karin sojoji zuwa yanki Abyei da ake rikici akai, domin karfafa ayyukan sintiri, da wasu ayyuka.
A farkon watan nan ne shugaban kudancin Sudan Salva Kiir, ya roki kwamitin sulhu a ta tura sojoji kan iyakar yankunan biyu domin shiga tsakani.
Menkerios yace, Majalisar Dinkin Duniya bata yanke shawara ko zata tura Karin sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Sudan ba. Yace ahalin yanzu aiki ya yi wa dakarun su duba 10 yawa.Ana samun karuwar zaman dar dar tsakanin kudanci da arewacin kasar, da gabatowar zaben raba gardama d a za’ayi ranar 9 ga watan Janairu.