Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Ya Ziyarci Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa a Abuja

Ziyarar Goodluck Jonathan da Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ganduje
Ziyarar Goodluck Jonathan da Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ganduje

Ziyarar tsohon shugaban dai ta janyo hasashe dabam daban daga 'yan Najeriya, game da tasirinta a irin wannan lokaci da kuma makomar siyasar kasar baki daya.

A wani al'amari mai daukar hankali, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai wa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ziyara a gidansa da ke Abuja.

Duk da cewa har yanzu dai ba a bayyana makasudin ziyarar ba, lamarin ya sa mutane da yawa ce-ce-ku-ce kan muhimmancin ziyarar a daidai wannan lokaci.

Jam’iyyar APC ta wallafa hotunan ziyarar a shafinta na manhajar X (twitter), inda ta rubuta, “Shugaban jam'iyya Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tarbi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan @GEJonathan a gidansa da ke Abuja."

Ziyarar Goodluck Jonathan da Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ganduje
Ziyarar Goodluck Jonathan da Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ganduje

Wani abin la'akari shi ne ziyarar ta zo ne bayan ce-ce-ku-cen da ke faruwa game da sukar da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bayelsa, Timipire Sylva yayi.

Sylva ya caccaki Jonathan kan kalamansa na mayar da mahaifiyarsa gida idan PDP ta fadi zabe a jihar.

Jonathan wanda ya taba zama jigo a jam’iyyar PDP, manazarta harkokin yau da kullum sun bayyana cewa yanzu za'a iya cewa tsohon shugaban na Najeriya, ya dan nesanta kansa da harkokin jam’iyyar PDP.

Ziyarar Goodluck Jonathan da Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ganduje
Ziyarar Goodluck Jonathan da Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa Ganduje

A yanzu haka dai al’amuran siyasa sun cika da hasashe dabam daban, inda 'yan Najeriya ke dakon abin da zai je ya dawo game da makomar siyasar kasar, da abin da ziyarar Jonathan ke nufi a irin wannan lokaci.

~Yusuf Aminu Yusuf.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG