Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido Ya Samu Beli


Sule Lamido sanye da farar riga yayinda ya samu beli daga kotu a Dutse babban binin Jigawa yau Alhamis
Sule Lamido sanye da farar riga yayinda ya samu beli daga kotu a Dutse babban binin Jigawa yau Alhamis

Tun makon jiya ne 'yan sanda suka kama Alhaji Sule Lamido daga gidansa dake Sharada cikin birnin Kano akan zargin da gwamnatin jiharsa keyi masa cewa yana harzuka mutane akan zaben kananan hukumomi da jihar ke shirin yi.

Tun da sanyin safiyar Alhamis din nan ne kotun ta zauna a cikin wasu tsauraran matakan tsaro a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ranar Talata lauyoyin dake kare Sule Lamido suka mika takardun neman belinsa bayan ya musanta tuhumar da gwamnatin jihar Jigawa keyi masa cewa yana yunkurin tunzura 'yan Jigawar game da zaben kananan hukumomin jihar dake tafe.

Alkalin ya karanto hujjojin da lauyoyin Sule Lamido suka bayar na neman belinsa. Lauyoyin sun ce yana da 'yancin a bada belinsa kamar yadda kundun tsarin mulkin Najeriya yayi tanadi.

Duk da sukar da lauyoyin gwamnatin jihar suka yi alkalin kotun yace kotun ta gamsu da dalilan da lauyoyin Sule Lamido suka gabatar. Kotun ta bada belinsa ba tare da gindiya masa wasu sharudda ba.

Mai Shari'a Usman Lamido yace kotun tayi la'akari da cewa Sule Lamido mutum ne mai mutunci a idon jama'a kuma ya rike mukamai da dama a kasar tare da zama gwamnan jihar har na tsawon shekaru takwas.

Kotun ta dage sauraran karar zuwa ranar biyar ga watan Yuli idan Allah ya kai rai.

Barrister Yakubu Abdullahi Ruba daya daga cikin lauyoyin dake kare Sule Lamido yace alkali yayi anfani da basirar sa, da shari'a yayi abin da dace. Yace zasu yi duk abin da zasu yi, domin tabbatar da an yi watsi da karar a karshe.

Su kuma lauyoyin dake kare bangaren gwamnati sun ce an basu umurnin kada su ce uffan akan maganar ga manema labarai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG