Tsohon dan Majalisar Wakilai Farouk Lawan ya shaki iskar 'yanci bayan da ya shafe shekaru 5 a gidan yari saboda nema da karbar cin hancin dala dubu 500 daga attajirin dan kasuwa Femi Otedola.
An sake shi daga gidan gyaran hali na kuje dake Abuja ne a yau Talata.
"Yau an bude sabon babi a rayuwata yayin da nake fita daga gidan gyaran hali na Kuje, ina mai matukar godiya ga Allah daya fidda ni daga wannan kangi," a cewar sanarwar daya fitar a yau.
Tsohon dan najalisar ya kuma godewa 'yan uwa da abokan arziki game da tallafawarsu a wannan lokaci na iftila'i a rayuwata."
"Ina matukar godiya, gashi ina raye cikin koshin lafiya da karsashin da zan kasance da 'yan uwa da abokai da dangina, bana daukar hakan da wasa," a cewarsa.
"Ba zan manta da gudunmowar da 'yan uwa da abokai suka bayar a wannan lokaci na iftila'i a rayuwata ba."
An same Lawan, wadda tsohon shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan tallafin man fetur ne, da laifi kuma aka yanke masa hukuncin dauri zuwa gidan yari a shekarar 2021.
Dandalin Mu Tattauna