TAKAFUL dai na gudana ne ba tare da karbar kudin ruwa ba inda a kan raba asara ko riba ga yadda kaddara ta zo.
“Raba wannan rara ta Naira miliyan 152 na nuna irin jajircewar wadanda suka shiga shirin da sadaukar ma na amanar dukiyar su” In ji shugabar majalisar daraktoci ta Ja'iz Takaful, Hajiya Zainab Abdulrahman a gagarumin taron raba rarar ga abokan hulda daga arewa da kudancin Najeriya.
Hajiya Zainab ta ce a kan ajiye kudin a bankin da ba a samun kudin riba kuma duk shekara za a duba hidimar da a ka yi da raba rarar kudi masu ajiya.
Da ya ke karin haske babban daraktan shirin Ibrahim Usman Shehu ya yi alwashin muradin saurin tura kudi ga masu ajiya a duk lokacin bukata ta taso “Idan wani abu ya samu kadarar da mu ka yi ma ka kariya a kai, mu na son mu biya ka a cikin sa’a 24.”
Bako mai jawabi tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Farfesa Isa Ali Pantami ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na iya cin gajiyar shirin don ba a cinikin biri a sama.
An mika takardun karbar kudi a banki ga wadanda suka samu rarar inda bankin ke cikin na kan gaba da samun Naira miliyan 18.
Abdulwahab Sadik jami’in bankin ne "A bara sun ba mu Naira miliyan 3.5 bana kuma abun mamaki sun ba mu Naira miliyan 18."
Wadanda suka assasa bankin da ba kudin ruwa a Najeriya irin su attajiri Alhaji Umar Mutallab, Sarkin Zazzau din Suleja Muhammad Auwal Ibrahim da Shehunan malaman Islama irin Sheikh Abdullahi Bala Lau sun halarci taron.
Zuwa yanzu akwai bankuna 3 da ke bin tsarin da ba riba a Najeriya da su ka hada da JAIZ, TAJ da LOTUS sai wasu da ke ba da damar haka ga mai bukata.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna