Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Majalisar Dattijan Amurka ta ce an yi kisan kare dangi a jihar Rakhine, Myanmar


Tawagar Majalisar Dattijan Amurka a Myanmar, shugaban tawagar Sanata Jeff Merkley shi ya yiwa 'yan jarida jawabi
Tawagar Majalisar Dattijan Amurka a Myanmar, shugaban tawagar Sanata Jeff Merkley shi ya yiwa 'yan jarida jawabi

Jihar Rakhine dake kasar Myanmar ita ce inda Musulmi 'yan kabilar Rohingya suke wadanda kasar Myanmar tace ba 'yan kasa ba ne har ta fara kashesu, dalili ke nan da tawagar Majalisar Dattawan Amurka ta kai ziyarar gani da ido kuma jiya Talata tace akwai alamun an yi kisan kare dangi a yankin

A jiya Talata, wata tawagar sanatoci daga Majalisar Dattawan Amurka da aka aike zuwa Myanmar, ta ce rikicin jihar Rakhine na dauke da wasu alamu da ke nuna cewa an aikata kisan kare dangi.

“Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijrar sun fuskanci cin zarafi da makusantansu, inda aka kashe musu yara da mazaje a gabansu, aka kuma yi wa matan aure da ‘yayansu fyade ko aka kona su ko kuma aka jikkata su. Wannan duk alamu ne na kisan kare dangi.” Inji Sanata Jeff Merkely na jam’iyar Democrat da ya fito daga jihar Oregon, yayin wani taron manema labarai da aka yi a ofishin jakadancin Amurka da ke Yangon.

Merkely ya fadawa manema labarai cewa, tawagar ta majalisar dokokin Amurka ta nemi gwamnatin Myanmar da ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin da Kofi Annan ya jagoranta ya bayar, sannan a kyale Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu su samu hanyar kai wa ga yankin da ake rikici, domin gudanar da ayyukan jin kai.

A nan Washington, Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, na duba yiwuwar saka wannan rikici na Myanmar a matsayin na kare dangi.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG