Tattaunawar da ake yi tsakanin Arewaci da Kudancin Sudan akan matsayin yankin Abyei da su ke takaddama akai na ci gaba da cijewa, hakan kuwa sama da mako daya bayan da shugabannin biyu su ka yi sanarwar cewa su na gaf da cimma yarjejeniya.
Za a ci gaba da tattaunawar har a yau litinin a birnin Addis Ababa a daidai lokacin da Arewaci da Kudancin Sudan ke kokarin warware manya-manyan matsalolin su kafin ballewar Kudancin Sudan a ranar 9 ga watan Yuli kamar yadda aka tsara. Amma ganin yadda tattaunawar ke kwan gaba-kwan baya, ana kara nuna fargaba game da sake fadawa cikin yakin basasa.
Mako daya kenan da shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir da shugaban Kudanci Salva Kiir su ka amince da gundarin kwashe sojojin su daga yankin Abyei mai arzikin man fetur su kuma bada dama a girka wata rundunar sojojin kasar Habasha masu kiyaye zaman lafiya a yankin. Sun yi hakan ne da nufin rattabawa jituwar hannu a wajen wani biki da yammacin ranar asabar.
Amma sai aka jinkirta bikin rattaba hannun kuma har a jiya lahadi tattaunawar ta na cije, a daidai lokacin da masu tattaunawa ke gardama akan yadda za a tabbatar da oda da karfafa bin doka bayan ayyana 'yancin kan Kudancin kasar. An ce bangarorin biyu na tsaurara matsayin su, kuma akwai labarin cewa masu tattaunawa na kara jin takaici saboda duk kokarin da su ke yi da nufin daidaita bangarorin biyu ya ci tura.
Haka ita ma jituwar tsagaita wutar kwanaki ukkun da aka cimma domin a bada damar isar da kayayyakin agajin da fararen hula ke matukar bukata a jahar Kudancin Kordofan, ta na fuskantar barazana sanadiyar kiki-kakar diflomasiyar.