Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma Zai Farfado a Bana


Ana sa ran sake farfadowar tattalin arziki a Afrika ta Yamma a cikin wannan shekara tun bayan shekaru 20 da tattalin arzikin yankin ya tabarbare ya zuwa shekarar 2016, a cewar wani rahoton Asusun lamuni ta kasa da kasa ta IMF da ta saba fitarwa a kowane shekaru biyu biyu.

Asusun IMF mai cibiya a nan Washington tayi gargadin cewa duk da farfadowar tattalin arzikin da ake hasashe, basussuka da gwamnatoci ke karba yana kara yawa kuma nan bada dadewa ba zai fi karfin wasu kasashen Afrika.


Bayan rauni da aka samu a shekarar 2016, yayin da tattalin arzikin yankin Afrika ta Yamma ya tashi da kashi daya da digo huda kacal, hukumar IMF tace ana sa ran samun farfadowar da kasha biyu da digo shida a wannan shekara kana ya tashi da kasha uku da digo hudu a shekarar 2018


Kashi daya cikin uku na tattalin arizikin wasu kasashen Afrika na samu bunkasa da kashi biyar. Amma dai Asusun IMF bata zaton sauran kasashen zasu kai ga wannan bunkasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG