Yayin da annobar corona ke cigaba da durkusar da ayyukan yau da kullum a fadin duniya, Najeriya ta fara fuskantar barazana a fannin tattalin arziki, inda tasirin faduwar farashin danyen mai ya sa gwamnatin tarayyar kasar ta fara nuna damuwa kan yadda gwamnatocin jihohi za su iya cigaba da biyan albashin ma’aikata a matakai daban-daban.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukar matakan bunkasa tattalin arzikin kasar ganin yadda annobar corona ke cigaba da yin barazana ga harkokin kasuwanci, inda ta fara zuba jari a bangaren cinikin albarkatun man fetur ta kan tudu a kasar.
A matakin jihohi, gwamnan jihar yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa tun da gwamnatinsa ta dare karagar mulki, an bada himma wajen tuntubar kwararru a fannin aikin noma domin karkatar da tattalin arzikin jihar saboda a samawa al’umar karkara ayyukan yi su dogaro da kai.
Ya kara da cewa, samun man fetur ya gurgunta aikin noma.
Kazalika, gwamna Mai Mala Buni ya ce gwamnatoci na shawara a kan bullo da dabarun tabbatar da cewa ana biyan albashin ma’aikata a lokacin da ya kamata.
Daga karshe dai, Mai Mala ya ce gwamnatinsa ta ayyana dokar ta baci a fannin ilmi, kuma kwararru na aiki domin farfado da bangaren ilmin.
Ga Halima Abdulrauf da cikakken rahoton:
Facebook Forum