Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin bam ya kashe mutum daya a Kenya


Ofishin Jakadancin Kenya
Ofishin Jakadancin Kenya

Fashewa yau juma'a a Nairobi baban birnin kasashen Kenya, ya kashe mutum daya, kwana kafin ziyarar da sakatariyar harkoki wajen Amirka zata kai birnin.

Fashewa a Nairobi baban birnin kasar Kenya a yau Juma'a, ya kashe mmutum daya, kwana daya kafin sakatariyar harkokin wajen Amirka ta kai ziyara birnin.

Wakili Muryar Amirka yace fashewar ta auke ne a sakamakon gazawar harin gurnati daga wata mota dake wucewa, to amma gurnatin ya fashe kafin a sako shi. Kuma kila maharin ne fashewar gurnati ta kashe.

Wani wanda yaga al'amarin ya fada cewa mahari yayi kokarin jefan wasu sojoji da gurnatin a cikin wata mota dake wucewa, amma gurnatin yayi bindiga kafin a sake shi.

Sananin yana unguwar Eastleigh, unguwar da yan gudun hijirar Somaliya da dama suke zaune a cikinta

Ana sa ran batu kasar Somaliya ya zama daya daga cikin batutuwan da Hilary Clinton zata tabo inda ta gana da shugaban Kenya Mwai Kibaki da Prime Ministan kasar Ra'ila Odinga a ranar Asabar.

Kasar Kenya tana daya daga ciki kasashen Afrika wadanda suka tura sojoji Somaliya suna fafatawa da yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab

XS
SM
MD
LG