Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi kasar Turkiyya cewa, tattalin arziki zai durkushe, muddun ta kuskura ta kai hari kan Kurdawa bayan janyewar sojojin Amurka a Siriya.
“Haka zalika, ba na son Kurdawan su tsokani Turkiyya,” a cewar Trump ta kafar twitter da daren jiya Lahadi.
Trump ya ce, “Kasashen Rasha da Iran da Siriya ne su ka fi amfana da dadaddiyar manufar nan ta Amurka ta ruguza ISIS – abokiyar gaba ta hakika.”
Dakarun Kurdawa na YPG na daya daga cikin abokan Amurka na kud-da-kud a yaki da ISIS a Siriya.
Turkiyya dai ta ce mayakan YPG na da alaka da kungiyar mayakan Kurdawa na PKK, wadda ta jima ta na yakin sunkuru na neman karin ‘yancin cin gashin kai ga Kurdawa a Turkiyya.
Turkiyya dai na daukar PKK a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, kuma akwai fargabar yiwuwar Turkiyya ta kai hari ma mayakan Kurdawa a Siriya da zarar Amurka ta fice.
Facebook Forum