Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Yi Iya Kokarinmu Mu Ga Cewa Mun Yi Abin Da Ya Kamata - Daurawa


Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hoto: Facebook/Hisbah)
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hoto: Facebook/Hisbah)

A ranar 1 ga watan Maris din shekarar 2024, Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Daurawa ya yi murabus daga mukaminsa kan kalaman na gwamna Abba Kabir Yusuf wadanda suka soki ayyukan da Hisbah ke yi.

Babban Kwamandan Hisbah a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sauka daga mukaminsa na jagorancin hukumar.

Kusan shekaru 22 da suka gabata aka kafa hukumar ta Hisbah a Kano don yin umarni da kyawawa da hani da munanan ayyuka.

"Mun yi iya kokarinmu, mu ga cewa muna abin da ya kamata, to amma ina ba mai girma gwamna hakuri bisa fushi da ya yi da maganganun da ya fada.

Ya kara da cewa, "kuma ina rokon a ya min afuwa, na sauka daga wannan mukami da ya ba ni na Hisbah..... inda muka yi kuskure muna fata a yafe mana." In ji Daurawa.

Yayin wani taro da limaman Kano a ranar Alhamis, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soki yadda hukumar ta Hisbah take gudanar da ayyukanta.

Gwamnan ya ce hukumar tana wuce gona da iri idan ta je kamen matasa maza da mata da ake zargi da aikata badala.

Abba ya ce hankalinsa ya tashi a lokacin da ya ga wani bidiyo da ke nuna yadda hukumar Hisbah take kama matasan tana dukansu tana jefa su cikin mota, matakin da ya ce ya wuce gona da iri.

A cewar gwamnan, bidiyon ya tayar masa da hankali. Kasa da sa'a 24 da kalaman na gwmna Abba, Sheikh Daurawa cikin wani bidiyo mai tsawon minti 2:53 ya sanar da murabus dinsa.

Sai dai kamar yadda wasu suka bayyana, murabus din Daurawa bai zo musu da mamaki ba, duba da cewa a ‘yan kwanakin nan an yi ta rade-radin cewa ya yi murabus dalilin wata takaddama da ta shafi wata fitacciyar matashiya ‘yar TikTok a jihar ta Kano da ake kira Murja Ibrahim Kunya mai shekaru 26.

Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Kamar yadda rahotanni suka nuna, a 'yan kwanakin nan batun Murja ya ja hankalin kusan kowa a jihar ta Kano da ma wajenta, bayan da hukumar ta kama ta amma kotu ta ba da umarnin a sake ta, lamarin da bai yi wa Daurawa dadi ba.

Ga yadda takaddamar Murja da Hisbah ta wakana:

  • A farkon watan Nuwambar 2023, Hukumar Hisbah ta gayyaci matasa – mata da maza masu amfani da shafin TikTok (har da Murja) don yi musu nasiha kan yadda ake zargin wasu daga cikinsu wajen dabbaka ayyuka na badala.

  • A ranar 24 ga watan Janairun 2024, hukumar Hisba ta sanar cewa tana neman wasu ‘yan TikTok shida ruwa a jallo ciki har da Murja Kunya bisa zargin su da wallafa bidiyo masu dauke da kalamai na batsa.

  • A ranar 13 ga watan Fabrairun 2024, hukumar Hisbah ta kama Murja da saurayinta kamar yadda Babbar Mataimakiyar Kwamanda Hisbah Dr. Khadija Sagir Suleiman ta tabbatarwa da Muryar Amurka. An kuma tura ta gidan gyara hali don jiran ranar 20 ga watan Fabrariru da za ta sake bayyana a gaban kotun. Murja ta musanta tuhume-tuhumen da ka mata.

  • A ranar 18 ga watan Fabrairun 2024 aka saki Murja, - kwana biyu gabanin ta sake bayyana a gaban kotu domin ci gaba da sauraren shari’arta. Hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce kan yadda aka saki fitacciyar ‘yar Tiktok din. Amma hukumar gidan gyaran hali ta Kano ta ce kotu ce ta ba da umarnin a sake ta. Sheikh Daurawa ya fito ya nuna rashin jin dadinsa kan sakin Murja inda ya yi nuni da cewa, “wanda ya fi karfin dokar Hisbah, ai bai fi karfin ta Allah ba.”

Murja Kunya (Hoto: Facebook/Murja)
Murja Kunya (Hoto: Facebook/Murja)
  • A ranar 20 ga watan Fabrairu, kotu ta ce a yi wa Murja gwajin lafiyar kwakwalwa duba da irin halayyar da ta nuna a lokacin zaman kotun da aka yi da ita da farko.

  • A ranar Alhamis 29 ga watan Fabrairu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soki yadda hukumar Hisba take kama matasan da ake zargi da aikata ayyukan badala bayan wani bidiyo da ya ce ya kalla – bidiyon da ya ce “ya tayar masa da hankali.”

  • A ranar 1 ga watan Maris, 2024, Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Daurawa ya yi murabus daga mukaminsa kan kalaman na gwamna Kabir.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG