Shugaban kungiyar tuntuba ta matasa da dattawan arewa, Northern youth and elders forum a Turance, Malam Mahmud Sani Yarima, ya ce aikin wannan kungiya ta su ya hada da fadakarwa da jajircewa wajen yada abin da zai kawo cigaba ga Arewacin kasar. Kuma wannan kudirin na su ne ma ya sa suka tsunduma ga harkar fim a Kannywood.
Ya ce, sun lura cewa mafi yawan masu harkar fim matasa ne. Sannan matsalolin matasa su ne abin dubawa. Sun lura da yadda suke gudanar da fina-finansu na fuskantar cibaya. Saboda haka suka ga cewa ya kamata a basu tallafi.
Ya kara da cewa sun fito da wani shiri na bada tallafi ga matasan arewa, wanda zai taimaka ma masana’antar kannywood ta hanyar bullo da gasa da bada kyautattuka ga wadanda su ke kokari a harkar ta fim. Misali kamar wajen rubutun fim ko shiryawa.
Mal. Mahmud ya ce suna da burin basu horo wajen inganta sana’arsu sannan suna so su ga suna karawa da takwarorinsu na Kudu wajen inganci fim ta fannin rubutun labari, kyaun hoto da sauransu.
Ya kara da cewa sun dauki masana’antar Kannywood domin a ganinsu masana’antar fim ta fi saurin isar da sako da tara jama’a. Hakan ce ta sa su ka mai da hankali a wannan fanni, sai dai ya bayyana cewa matsalar Kannywood ba abu daya ne musabbabinta ba. Don haka ne ma ya ga ya kamata a tallafa musu ta hanyar shirya masu taron bita, kuma zai taimaka wa masana’antar ta sauran wasu hanyoyin.
A yanzu dai su na neman tallafi daga gwamnatocin arewa da sauran al'ummar gari, domin cimma wannan muradi nasu.
Facebook Forum