Wata kotun tarayya dake zama a Ibadan, ta yakewa miji da mata daurin shekaru goma sha hudu a gidan yari, batare da bada zabin tara ba.
Kotun dai ta sami wadannan maurata biyu ne masu suna Idowu Folorunso mai shekaru talatin da bakwai, da matar sa Titilayo, da laifin fataucin mutane ne.
Mai shara’a Joyce Abdulmaleek, tace mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu na bakin da kuma a rubuce da kotu ta gamsu dasu.
Idowu da Titilayo, sun yiwa Bidemi Adeshina, karyar cewa akwai aikin koyarwa a kasar Libiya, saboda haka ta yi amfani da damar zuwa Libya, ta kuwa bi umarninsu zai daga bisani abin ya kasance aikin karuwanci ne.
Da take bada ba’asi tun farko Bidemi Adeshina, tace miji da matar sun yaudareta ne suka jefa ta a harkar karuwanci a kasar Libiya, gashi yanzu tana dauke da kwarai cutar HIV.
Ta kara da cewa a cikin watani takwas sun sa ta zubar da ciki har sau hudu, kuma basu bata kudi daga abinda aka samu a karuwancin ba.