Rundunar sojan Sudan ta lashi takobin murkushe yan tawaye da take zargi da laifin kashe jami’an gwamnati guda biyu da wasu mutum shidda a kwantar baunar da su ‘yan tawayen suka yi a ranar juma’a, a yayinda ta baiyana kisan a zaman cin amana.
Kamfanin dilancin labarun Sudan da ake cewa SUNA a takaice ya bada labarin cewa yan tawayen sun kasha kakkakin Majalisar gudanarwa jihar Kordofan ta arewa Ibrahim Balandiya da kuma wani dan Majalisar dake kula da dabaru da kuma tsare tsare Faisal Bashir.
Rundunar sojan Sudan ta dorawa kungiyar yan tawaye Sudan Peoples Liberation Movement North ko kuma SPLM a takaice laifin kisan, zargin da kungiyar yan tawayen ta musunta.
Fiye da shekara guda ke nan, kungiyar yan tawayen ta SPLM ke fafatawa da sojojin Sudan a jihar Kordofan ta arewa da kuma jihar Blue Nile dake kan iyakar kasar da Sudan ta kudu. Kungiyar yan tawayen ta goyi bayan Sudan a yakin basasar shekaru ashirin da biyu data fafata da kudancin kasar.