Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu ta yi sabon mataimakin shugaban kasa


Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir.

hugaban ‘yantattar sabuwar kasar Sudan ta Kudu ya zabi mataimakin shugaban kasa ya kuma kafa gwamnatin rikon kwarya. A dokar da ya kafa jiya Lahadi, shugaba Salva Kiir ya zabi Reik Machar a matsayin mataimakinshi.

Shugaban ‘yantattar sabuwar kasar Sudan ta Kudu ya zabi mataimakin shugaban kasa ya kuma kafa gwamnatin rikon kwarya. A dokar da ya kafa jiya Lahadi, shugaba Salva Kiir ya zabi Reik Machar a matsayin mataimakinshi. Machar ya rike wannan mukamin a tsohuwar gwamnatin yankin kudancin Sudan. An rantsar da shi yau Litinin. A wata doka dabam, shugaba Kiir ya zabi ‘yan majalisa wadanda sanarwar da gwamnati ta bayyana a matsayin ministocin wucin gadi. An sanar da Nhial Deng Nhial a matsayin ministan harkokin kasashen ketare, yayinda aka ba Pagan Amum ministan aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ta shekara ta dubu biyu da biyar da ta kawo karshen yakin basasa tsakanin arewaci da kudancin Sudan, da ake kira CPA. Sabanin ra’ayi dangane da yarjejeniyar ya kara sa dangantaka tayi tsami tsakanin Sudan da kuma Sudan ta Kudu, ko da yake gwamnatin Khartoum ta amince da diyaucin Sudan ta Kudu. A cikin hirar da aka yi da shi jiya Lahadi, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya bayyana cewa, za a kai ruwa rana a kan yankin Abyei mai arzikin man fetir idan ta kama. Sai dai ya shaidawa tashar BBC cewa, ya yi na’am da tura dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Habasha wadanda suke kokarin kiyaye zaman lafiya a yankin dake fama da tashin tashina.

XS
SM
MD
LG