Gwamnatin sojin kasar Sudan, ta dakatar da tattaunawar da take yi tsakaninta da shugabannin fararen hula masu zanga-zanga, kan batun gwamnatin wucin-gadi, bayan da aka raunata akalla mutane 8 a wani rikici da aka yi da jami'an tsaro a birnin Khartoum jiya Laraba.
A yau Alhamis, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya bayyana cewa, an dakatar da tattaunawar har na tsawon sa'o'i 72, sanadiyyar harbe-harben da aka samu, wanda ya dora laifi akan masu zanga-zangar da suka ki cire shingayen da suka saka a manyan hanyoyin babban birnin kasar.
A farkon watan da ya gabata ne aka dasa wadannan shingayen, a lokacin da aka fara zaman dirshan, wanda ya jirkice ya koma zanga zangar neman dadadden tsohon shugaban kasar mai mulkin kama-karya, Omar al Bashir ya sauka daga mulki.
A ranar 11 ga watan Afrilu, sojoji suka kawo karshen mulkin Al Bashir, amma duk da haka, masu zanga zangar suka bijire suka ki kawar da shingayen tare da ci gaba da zaman na dirshan, suna neman sojojin su mika mulki ga gwamnatin farar hula.
Facebook Forum