Kocin riko na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ba ya bukatar kammala zamansa a karshen kakar wasa mai zuwa da kungiyar.
Manchester United dai na tare da kocinne a matsayi na rukon kwarya, bayan da ta sallami Jose Mourinho a watan Disambar 2018, bisa yarjejeniyar zuwa karshen kakar wasan bana zata nada kocinta na din din din.
A ranar Laraba, da ta gabata kungiyar ta samu nasarar doke takwararta Newcastle daci 2-0 a wasan firimiya lig mako na 21.
Hakane ma yasa kocin ya zama mai horas da 'yan wasa na biyu a tarihin kungiyar da ya samu nasarar lashe wasanni hudu a jere ba tare da an doke taba, tun a alif 1946 kimanin shekara 72 lokacin Sir Matt Busby, wanda ya
ci gasar lig biyar tsakanin shekarun 1945 zuwa 1969 da kuma 1970 zuwa 1971.
Yayin da yake jawabi wa 'yan jaridu Solskjaer yace baya son barin kungiyar a karshen kakar bana cikin watan Mayu 2019, kamar yadda akayi alkawari da kungiyar da yake horaswa Molde na kasar Norway, kafin yazo Manchester United.
Kungiyar ta Molde ta bayyana cewa tana sa ran kocinta zai dawo bayan kammala zaman aro da yakeyi a United. Solskjaer ya ce: yanzu abunda yake gabansa shine, "ina tunanin wasan mu na gaba ne, wannan kalubale ne a gare mu, kuma dama mun saba fuskantar irin wannan kalubalen."
Manchester dai tana matsayi na shida ne da maki 38 banbancin maki 3 kacal tsakanita da babbar abokiyar hamayyata Arsenal, wace take matsayi na biyar da maki 41.
Facebook Forum