Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solkjaer, ya ce dan wasan tsakiya na kulob din Paul Pgoba, ya na bukatar tiyata a kafarsa, sakamakon wani rauni da ya samu a idon sahunsa.
Manajan ya ce dan wasan zai shafe akallah makwanni uku zuwa hudu, kafin ya dawo filin wasa.
Pgoba bai sami damar buga wasan da Arsenal ta doke Manchester United da ci 2-0 ba, a wasan mako na 21 a gasar Firimiya lig na bana, wasan da aka yi jiya Laraba 1 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2020.
A watan da ya gabata ne dan wasan, dan kasar Faransa ya dawo daga jinyar rashin lafiyar da yayi fama da ita tun a watan Satumban bara.
Solkjaer ya ce binciken da aka yi, ya nuna cewa raunin da ya samu ba mai tsanani bane, amma ya kamata a dauki matakin magance shi da wuri.
Wasanni takwas kawai Paul Pgoba ya bugawa kungiyar a bara, bayan an yi masa tiyata ta farko a raunin da ya samu a gwiwar sa.
Kocin kungiyar ya yi fatan dan wasan zai sami sauki cikin wata guda bayan an yi masa aiki.
Facebook Forum