Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kasar Ukraine na Cikin Shirin ko ta Kwana


Sojojin Ukarine a Mariupol, Ukarine, 15 ga Satumba, 2014.
Sojojin Ukarine a Mariupol, Ukarine, 15 ga Satumba, 2014.

Firayim Ministan Ukraine ya yi kira ga sojojin kasar a yau Laraba, da su cigaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana, duk kuwa da yarjajjeniyar tsagaita wutar da aka cimma a gabashin Ukraine.

Firayim Ministan Ukraine ya yi kira ga sojojin kasar a yau Laraba, da su cigaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana, duk kuwa da yarjajjeniyar tsagaita wutar da aka cimma a gabashin Ukraine, a yayin da wani barin wuta da aka yi a birni mafi girma na yankin, ya yi sanadin mutuwar fararen hula biyu.

Firayim Minista Arseniy Yatsenyuk ya fadi a wani taron Ministoci cewa a yayin da ake bukatar tabbatar yarjajjeniyar tsagaita wutar da aka rattaba hannu akai a ran 5 ga watan Satumba don a tsai da fadan da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da 'yan aware masu ra'ayin Rasha, Ma'aikatun Tsaro da na Cikin Gidan Ukarine ba za su yi sake ba saboda, a ta bakinsa, "Ko muskalazaratun Rasha ba za ta ba mu kwanciyar hankali da lumana ba."

NATO ta fadi jiya Talata cewa sojojin Rasha kimanin 1,000 na cigaba da zama a gabashin Ukraine. Yawancin masu lura da al'amura na ganin shiga kai tsaye da sojojin Rasha su ka yi, shi ya sa reshe ya juye da mujiya a fadan da sojojin na Ukraine ke yi da 'yan awaren.

A halin da ake ciki kuma, jami'an hukuma a birnin Donetsk da ke gabashin Ukraine da ke karkashin ikon 'yan tawaye sun ce wasu fararen hula biyu sun mutu wasu kuma uku sun samu raunuka a yau dinnan Laraba, a wani barin wutan da ya addabi wata unguwa. Yawan mace-macen fararen hula na ta karuwa duk kuwa da yarjejjeniyar tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG