Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Ouattara Da Na majalisar Dinkin Duniya Sun Kai Hari Kan Sojojin Gbagbo


Wuta da hayaki na tashi daga sansanin soja na Akouedo a Abidjan, bayan da sojojin Majalisar Dinkin Duniya suka kai masa farmaki litinin 4 Afrilu 2011.
Wuta da hayaki na tashi daga sansanin soja na Akouedo a Abidjan, bayan da sojojin Majalisar Dinkin Duniya suka kai masa farmaki litinin 4 Afrilu 2011.

An ci gaba da gwabza kazamin fada yau talata a Abidjan, yayin da mayakan Ouattara suka kaddamar da farmakin karshe na tumbuke Laurent Gbagbo

An ci gaba da gwabza fada yau talata a yayin da aka ji kararrakin harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da fadar shugaban kasa a Abidjan, birni mafi girma na kasar Ivory Coast.

Sojoji masu goyon bayan Alassane Ouattara, mutumin da kasashen duniya suka yi na'am da shi a zaman shugaban kasa, sun nausa suka doshi wurare kalilan da suka rage a hannun shugaba Laurent Gbagbo, a yayin da suek kokarin kawar da shi.

Ofishin kula da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast ya fada a jiya litinin cewa jiragen saman helkwafta na majalisar sun kai farmaki kan wasu sansanonin soja biyu na Gbagbo, da fadar shugaban kasar da kuma gidan Mr. Gbagbo.

Faransa ta ce mayakanta sun sa hannu a kai farmakin bisa rokon Majalisar Dinkin Duniya. Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya umurci sojojin Faransa da su kare fararen hula su kuma kawar da manyan makamai na Mr. Gbagbo.

Magoya bayan Gbagbo sun ce hare-haren da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Faransa suka kai na haramun ne, kuma yunkuri ne na kashe shugaban dake kan mulki.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace an kai hare-haren ne domin hana yin amfani da bindigogin harba kwanson bam da wasu manyan makamai a kan fararen hula da sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar. Yace wadannan matakan sojan ba wai su na nufin cewa majalisar tana kai farmaki kan Gbagbo ba ne.

XS
SM
MD
LG