Zaratan Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa mai kula da Shiya ta 1 a shiyar Arewa Maso Gabashin Najeriya mai lakabin "Operations Hadin Kai" ne suka kubutar da mutanen 387 da suka hada da mata da kananan yara
Dakarun, karkashin jagorancin Burgediya Janar Diwa, sun yi nasarar kwato ababen hawa da makaman da a baya 'yan taaddar suka kwata daga hannun dakarun Najeriya a ganiyar rikicin Boko Haram.
Da yake marabtar dakarun Kwamandan Shiya ta 1, Abubakar Haruna yace kodai 'yan taaddar su mika wuya ko kuma su fuskanci mutuwa kasancewar an lalata dukkanin maboyarsu.
A cewar Haruna, karshe dai aikin da aka tsara kammalawa cikin kwanaki 4 ya kai kwanaki 10.
Daya daga cikin matayen mayakan Boko Haram mai suna Hajara Danjuma tace mijinta na daga cikin wadanda suka fara shiga kungiyar.
Tare da mukaman da aka kwato, anyi safarar iyalan mayakan Boko Haram din da aka kubutar zuwa shelkwatar rundunar sojin dake birnin Maiduguri akan hanyarsu ta zuwa shelkwatar sojan Najeriya dake Abuja.
Dandalin Mu Tattauna