Yanzu haka dai jami’an tsaron Najeriya, sunyi rawar gani inda suka samu nasar kwato kusan duk kananan hukumomi da ke karkashin ‘yan kungiyar boko haram. Kimanin sama da watanni da dama kenan ‘yan kungiyar ta boko haram suka mamaye wasu garurwa a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, amma yanzu jami’an tsaro na iya kokarin su wanda yanzu haka su kasa mu nasarar kwato shida daga cikin kananan hukumomi bakwai da ‘yan ta’adda suka kame.
Yanzu ma haka dai hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Adamawa, tabakin sakataren hukumar Alh. Haruna Hamman Fure, yayi muna Karin haske dangane da halin da ake ciki a wadannan garuruwan, inda yace suna kokarin kai kayan agaji ga duk al’umar dake wannan yanki don taimaka musu, su cigaba da rayuwasu mai inganci.
Ta bakin Dr. Bawa Abdullahi Wase, yana ganin dama wannan wani abune da gwamnati ta tsara, ganin cewar tun shekaru da suka gabata ba tayi wani abu ba dangane da wannan abun ba sai yanzu da taga zabe yakawo jiki, suna kuma yin wannan ne don cinma wani burinsu na daban. A bangaren gwamnati kuwa suna gani kamar ba haka abun yakeba, ta bakin Mr. Mike Omeri, shugaban cibiyar bada bayanai don yaki da ta’addanci a Nigeriya, yace gwamnati na iya kokarinta don ganin an samu zaman lafiya a wannan garuruwan. Ya kuma kara da cewar yakamata mutane su gujema yada jita jita saboda wannan zai iya haifar da rashin zaman lafia a kasar baki daya.