Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Ruwan Amurka Zasu Tura Naurar Gano Baraguzen Jirgin Ruwan Dakon Kaya da Ya Bace


Jirgin ruwa
Jirgin ruwa

Amurka na shirin tura naura mai shiga karkashin kasa daz ai gano baraguzen jirgin dakon kaya mai suna El-Faro da ya bace watan jiya.

Rundunar sojin ruwa ta Amurka tana shirin tura na'ura mai shiga karkashin ruwa domin tantance ko baraguzan jirgin ruwa da aka gano kusa da Bahamas, na jirgin dakon kayan nan ne mai suna El-Faro, wanda ya bace lokacin da aka yi wata mahaukaciyar guguwawatan jiya.

Ana sa ran rundunar ta fara aikin tun jiya Lahadi, kamar yadda aka gani cikin wata sanarwa da hukumar kula da lafiyar zirga zirga ta Amurka ta bayar.

Jirgin mai tsawon kafa 790 ya bace ne a farkon watan jiya da ma'aikata 33 a cikinsa, lokacinda mahaukaciyar guguwar da aka lakabawa suna Joaquin ta fatattaki yankunan.

Hukumomi suka ce suna shirin suyi safiyon baraguzan da zummar gano akwatin tara bayanai na jirgin, wanda ake fatan zai samarda bayanai kan abunda ya faru.

Idan sun gano gawarwakin mutane lokacinda suke tantance baraguzan, sojojin ruwan na Amurka za su yi kokarin su fitarda su, kamar yadda kakakin hukumar kula da lafiyar zirga zirgan ababan hawa na Amurka Peter Knudson ya fada.

Matukin jirgin ya aike da sakon neman-doki cewa injinan jirgin ruwan sun daina, aiki kamin jirgin ya bace, yayinda yake kan hanyarsa daga Jacksonville Florida zuwa San Juan, Puerto Rico.

XS
SM
MD
LG