Sojojin Amurka na neman wasu nau'ukan mutum-mutum na inji ba don fada ba, sai don taimaka wa dakarunta wajen aikin tsaro.
A gani na na’urorin za su taka muhimmiyar rawa ta fuskar yaki, cikin shekaru goma ko goma da rabi masu zuwa
Na’urorin dai ba makamai ba ne, amma an yabi kamfanonin da ke kera irinsu. Kwangilar da za ta ci dalar Amurka miliyan 500 za ta samar da matsakaitan mutum-mutum na inji guda 3,000 domin kare harin bam da kuma gano mabuyar 'yan ta’adda. Mahawara akan ayyukan ya karade har majalisa da kotun tarayya.
Kwararre a fannin tsaro na zamani da ke wata cibiyar soji ta Amurka wato Centre for New American Military, Paul Scharre, ya ce aikin Samar da mutum-mutum na inji da ma wasu ayyuka zai taimaka wa jami'an tsaro wurin gano abokan gabansu da ke boye, yana mai cewa nau'ukan mutum-mutum na inji za su taimaka wa aikin tsaron.
Babbar gasa kan kananan nau'ukan mutum-mutum na inji ita ta bude kofar fasahar zamani da tsaron kasa. Akwai kuma fargabar cewa kasar Sin za ta sha gaban Amurka ta wannan fanni na kere-keren zamani, tana kuma amfani da kananan fasahohi da manhajoji wajen gurgunta abokan gasarta. Akwai kuma batun ko za a takaita samar da fasahohin tsaro na zamanin ga kamfanonin Amurka kadai, domin kauce wa fadawarsu hannun abokan gaba.
Ko da kuwa wadanne kamfanoni ne ake da su wurin samar da mutum-mutum na inji, har yanzu akwai mahawara akan samar da na'urar, duk da ma mutum-mutum na injin ba wani sabon abu bane a wajen jami'an tsaro. Da farko dai, rundunar sojojin ta yi shirin samar da mutum-mutum na inji iri daban-daban har guda dubu biyar (5,000). Haka kuma, rundunar sojojin ruwa, da na sama na kokarin samar da ire-iren wadannan na'urori.
Hafsan Sojojin Amurkan, General Mark Milley, da ya ke jawabi a watan Mayun da ta gabata a wani zaman majalisar kasar, ya ce “A gani na na’urorin za su taka muhimmiyar rawa ta fuskar yaki, cikin shekaru goma ko goma da rabi masu zuwa” ya kuma bukaci karin kudade domin zamanantar da sha’anin tsaron.
Facebook Forum