Samson Siasia, tsohon dan wasan Najeriya kuma manajan Super Eagles, ya zargi hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF da gaza taimaka masa wajen yakar takunkunmin da hukumar FIFA ta sanya masa a watan Agusta.
FIFA ta sanya takunkumi ne ga “duk wasu ayyukan da suka shafi kwallon kafa (na gudanarwa, wasanni ko wasu) a matakin kasa da kasa” sannan kuma ta ci tarar wannnan dan wasa $ 50,000.
Takunkumin ya samo asali ne daga wani babban binciken da hukumar FIFA ke gudanarwa kan halayyan Wilson Raj Perumal, wanda aka taba kamawa da cogen shirya sakamakon wasannin kuma dan kasar Singapore.
A wata sanarwa da tsohon dan wasan Nantes da Lokeren ya aika wa wakilin a ranar Litinin, Siasia ya ce ya ji "kamar an yi banza da shi" tun lokacin da FIFA ta sanya takunkunmin da ya bata aikinsa, saboda hakan yana hana shi samun kudi daga kwallon kafa.
Siasia ya ce "Ni da iyalina mun yi takaicin cewa Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya (NFF) da sauran hukumomin gwamnatin Najeriya har yanzu (duk da alkawurra) sun kasa taimaka mun." In ji Siasia.
"Babu abin da aka yi. Na yi roko ga ‘yan Najeriya, da jami’an Gwamnatin Tarayya, da Majalisar Wakilai ta kasa, da ma’aikatun tarayya, da mutanen kirki da masu kaunar wasanni, da kuma Nijeriya baki daya. Duk da haka, ban sami wani babban taimakon kirki ba, sai daga mutane biyu da ke kusanci da ni da abokan arziki da suka kasance tare da iyalina har zuwa yau, ”in ji Siasia da ya ke korafi.
“Ya Najeriya, a ina kike a lokacin bukata na? Na yi imanin cewa saboda FIFA ta san cewa mu 'yan Najeriya ba ma kula da namu ... za ta yi tunanin cewa ai ba abun da zai faru game da kawar da kuskuren takunkumin), saboda babu wani matsanacin matsin lamba da za ta fito daga Najeriya, " korafin da Siasia ya ci gaba da yi kenan.
Siasia, wanda ya jagoranci Najeriya wajen ciyo lambobin azurfa da tagulla a wasannin Olimpics na 2008 da 2016 a Beijing da Rio, ya kuma zargi FIFA da toshe duk wata hanyar da za a bi wajen daukaka kara.
Facebook Forum