Mujallar nan da ake kira Time Magazine, ta ayyana shugabar kasar Jamus Angela Merkel, a zaman "zakarar shekara ta 2015. Mujallar tayi la'akari da shugabancinta a lokacinda ake fuskantar matsalar 'yan gudun hijira daga Syria, matsalar ceto tattalin arzikin Girka, da matsalar kudi da kasashe dake Tarayyar Turai suka fuskanta, da kuma kan katsalandan da Rasha tayi a Ukraine.
Mujallar Time tace, duk lokacinda Turai ta fuskanci matsala ko damuwa nan-da-nan shugaba Merkel zata shigo kuma a sami maslaha.
Editar mujallar Nancy Gibbs, ta rubuta jiya Laraba cewa, ana sanin karfin shugaba, a dai dai lokacinda al'uma suke turjiya, a irin wadanan lokutan ne inji Gibbs, Merkel take shigewa gaba da karfin halin shugabancin da ake karancinsa a duniya baki daya.