Shugabannin Kungiyar tarayyar Turai sun bada cikakken goyon bayan su ga kasar Birttaniya akan zargin da tayi wa kasar Rasha nayin anfani da sindari mai guba wajen kashe wani tsohon mai liken asiri,Sergei Skiripal shi da diyar sa Yulia a kudancin Ingila a wani lokaci cikin wannan watan.
Wadannan mutanen dai da wannan lamari ya rutsa dasu sun kasance cikin mawuyacin hali a asibitin da aka kaisu, haka shima dan sandan dake wurin sailin da abin ya faru kuma ya shafe shi sai a ranar alhamis ne aka sallamo shi daga asibiti.
Da take Magana jiya Jumaa a taron na kungiyar Tarayyar Turai, Prime MInistan Birtaniya Theresa May ta godewa daukaci kasashen da suka bata wannan goyon baya akan Rasha.
May ta shaidawa manema labarai cewa wannan danyen aikin da Rasha ta aikata ba barazana bace kawai ga kasar Birtaniya a’a harma da sauran kasahe.
Sai dai Jakadar na kasar ta Rasha a wannan kungiyar an umurce da ya koma gida a matsayin wani nuna kin amincewa da wannan matakin da wadannan kasashen suka nuna na goyon bayan Birtaniya akan wannan batu.
Yanzu haka dai wasu kasashen na wannan kungiyar kamar su Lithuania,Poland da Denmark suna duba yiwuwar daukar matakin sallamar jakadun Rasha dake kasashen su.
Yayin da Germany da Farance suke duba yiwuwar daukar matakin fiye da sallamar jamian diflomasiyyar kasar ta Rasha.
Angela Merkel tace mun fada da babban murya cewa muna kallon wannan a wani babban kalubale ne a gare mu dama tsaron kasashen mu.
Facebook Forum