Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma suna taron kungiyar ECOWAS domin nazartar halin da ake ciki a kasar Mali. An kiyasta cewar sabon rikici a tsakanin ‘yan tawayen Abzinawa da msu kishin Islama ya janyo asarar rayukan mutane akalla ashirin.
Shi wannan zaman taron gaggawa na ECOWAS, zai kuma nazarci matsalar harkokin tsaron da ake fuskanta a dalilin juyin mulkin soja a kasar Guinea Bissau. Tashin sabon rikici a kasar Mali zai tilastawa kungiyar ECOWAS daukan matakin tura sojin kiyaye zaman lafiya cikin gaggawa domin hana rikicin watsuwa.
A tattaunawar da Darektan hulda da yada labarai na kungiyar ECOWAS yayi da Muryar Amurka, Sonny Ugoh ya musanta zargin da ake yiwa kungiyar na kasa tabukan komai kan rikice-rikcen dake neman bazuwa a Afirka ta yamma inda yake cewa:
Yana ganin shugabannin kasashen Afirka ta Yamma na iyakar kokarinsa wajen tattauna hanyar kawo karshen rikicin da ake yi a kasar Mali, kuma yana bada tabbacin cewa za’a kokarta gano hanyar warware sauaran rikice-rikicen yankin na Afirka ta yamma.