Shugabanin jam’iyar a jihar sun yi Allah wadai da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka,yayin da wannan batun tuni ya raba kawunan yan siyasar jihar.
Tun bayan da mukarraban gwamnan jihar Adamawa Bindo Jibrilla suka jangwalo wannan batu na cewar gwamnati da kuma al’umman jihar ,tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne suke so kuma za’a mara masa baya don zama shugaban kasa a shekarar 2019,batun da yanzu haka ke cigaba da jawo martani da kuma cece-kuce.
Jihar Adamawa dai ,jihar da uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ta fito jiha ce dake da rikakkun yan siyasa da aka dade ana fafatawa dasu,wadanda sau tari kuma rikicin siyasar jihar kan rikida ya koma na kasa baki daya.
To sai dai kuma a karon farko,jam’iyar APC dake mulkin jihar ta tsame kanta game da wannan nuna goyon baya da gwamnatin jihar ta nunawa tsohon mataimakin shugaban kasan Atiku Abubakar.
Jam’iyar APCn ta bakin sakataren ta a jihar Adamawan Alhaji Saidu Nera,ta yi Allah wadai da kalaman mukarraban gwamnan jihar.
To sai dai yayin da jam’iyar ke wanke kanta,wasu yayan jam’iyar irinsu Hon.Hussaini Gambo Bello, shugaban yan shinkafa na jam’iyar APC yace suna kan bakansu na cewa sai Atiku.
Ko da yake kawo yanzu Atiku bai fito karara ya bayyana matsayinsa ba,to amma a wancan taron da hadiman gwamnan suka fasa kwai,tsohon mataimakin shugaban Najeriya ,yace shi burinsa shine kawo cigaba.