Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya yi kira da a tura dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa zuwa kasarsa, bayanda ya umarci dubban sojojinsa su janye daga garin Debaltseve da
‘yan aware da Rasha ke marawa baya suka kwace.
Ofishin Mr. Poroshenko ya bayyana jiya Laraba cewa, wani taron majalisar tsaron kasar da shugaban kasar Ukraine ya jagoranta, ya tsaida shawarar yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta tura dakarun wanzar da zaman lafiya, da zasu yi aiki karkashin dokokin kwamitin sulhu na majalisar.
Wannan yazo ‘yan sa’oi bayanda dubban dakarun kasar Ukraine suka arce daga Debaltseve, wani wuri mai muhimmanci da ya hada yankin dake karkashin ‘yan tawaye Luhansk da Donetsk.
‘Yan tawayen sun kama daruruwan dakarun gwamnati suka kuma yiwa wadanda basu kama ba kawanya, suka katse hanyoyin samun ruwa da abincinsu.
Fadar White House ta bayyana jiya Laraba cewa, a fili yake karara cewa, Rasha da ‘yan awaren gabashin Ukraine basu kiyaye yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma makon da ya gabata ba a Minsk, kasar Belarus.Shugaba Obama ya kuma yi gargadin cewa, wannan yana iya janyo masu wata babbar asara.
A ganawarsa da manema labarai, Kakakin fadar white House John Earnest yace ya kamata suyi taka tsantsan da matakin da zasu dauka gaba. Ya kara da cewa, gwamnatin shugaba Obama ta hakikanta cewa, za’a iya warware rikicin da zamantattaunawa.
Kazalika jiya Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki tace Washington bata fidda zuciya a kan nasarar yarjejeniyar da aka cimma ba a Minsk ta tsagaita wuta a Ukraine , sai dai ta damu matuka kan rahoton dake nuni cewa, ‘yan aware suna cigaba da kai hari kan Debaltseve tare kuma da keta yarjejeniyar tsagaita wutar a wadansu wurare.
Psaki tace sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Kerry ya yi magana da takwaransa na kasar Rasha Lavrov ya kuma yi kira da a shawo kan hare haren da ‘yan aware suke kaiwa.
Shugabannin kasar Faransa,Jamus,Britaniya da Italiya wadanda suka taimaka wajen tsaida yarjejeniyar tsagaita wutar, sun bayyana jiya cewa yarjejeniyar tana nan daram.