Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sami lambar yabo kan yaki da Polio


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Kulob din Rotary ya ba shugaban Najeriya Goodluck Jonathan lambar yabo domin kokarinshi a yaki da cutar shan inna.

Kulob din Rotary ya ba shugaban Najeriya Goodluck Jonathan lambar yabo domin kokarinshi a yaki da cutar shan inna.

Da yake jawabi a wajen bukin da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja, shugaban kulob din Rotary, Wilfred Wilkinson ya ce an ba shugaba Jonathan lambar yabon ne sabili da hazakar da ya nuna a yaki da cutar shan inna a Najeriya.

Bisa ga cewar Wilkinson, An sami raguwar yaduwar kwayar cutar shan inna da kimanin kashi 95% a shekara ta dubu biyu da goma sakamakon sabon salon da shugaba Jonathan ya dauka na yaki da cutar.

Mr. Wilson ya bayyana cewa, binciken da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da goma sha daya a Najeriya ya nuna cewa, cutar tana ci gaba da barazana ga nasarar da aka cimma cikin shekarar da ta gabata. Yace kulob din ya ba shugaba Jonathan lambar yabon ne ganin matakin da ya dauka na kafa kwamitin gudanarwa da nufin yaki da cutar.

A cikin jawabinshi, shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana godiya da karamcin tare da alkwarin ganin bayan cutar nan da shekara ta dubu biyu da goma sha biyar. Shugaba Jonathan yana mai cewa, “alkawarin da nayi wa kowanne karamin yaro a Najeriya da uba da kuma uwa shine, ko da ba zamu iya shawo kan matsalolin lafiya ba, wannan gwamnatin ta kuduri aniyar kawar da cutar shan inna a kasar kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.”

Shugaba Jonathan yace, ya umarci ministan lafiya ya sa ido sau da kafa domin ganin nasarar shirin. Ya kuma yiwa kulob din Rotary alkawari cewa, zai hada hannu tare da su da kuma sauran wadanda abin ya shafa domin kawar da ciwon shan inna.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma sanar da kara kudin yaki da cutar shan inna daga dala miliyan goma sha bakwai da aka kiyasta kashewa zuwa dala miliyan talatin, tare kuma da alkawarin kara kudin nan gaba idan bukatar yin haka ta tashi.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG