Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban masu hamaiya a kasar Kenya ya yi watsi da sakamakon zabe


Kenya's opposition leader Raila Odinga makes a statement to the media in Nairobi, Oct. 31, 2017.
Kenya's opposition leader Raila Odinga makes a statement to the media in Nairobi, Oct. 31, 2017.

Shugaban masu hamaiya a kasar Kenya Ra'ila Odinga ya baiyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a zaman shirme

Yau Talata shugaban ‘yan hamaiyar kasar Kenya Ra’ila Odinga ya baiyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a zaman shirme. Wannan ne furucin farko da Mr Odinga yayi tun lokacinda hukumar zaben kasar ta ayyana cewa shugaba Uhuru Kenyatta ne ya lashe zaben.

A jawabin daya gabatar ta gidan talibijin kasar, Mr Odinga yace masu hamaiya zasu bukaci magoya bayansu su kauracewa kashe kudadensu, domin kassara tattalin arzikin kasar, zasu kuma yi amfani da wasu hanyoin nuna rshin amincewa ta halal ciki harda yin jerin gwano ko kuma yin zanga zanga cikin lumana domin yin watsi da sakamakon zaben.

Bai baiyana ko zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu ba

A yayinda yan takara guda takwas aka baiyana akan takardar zabe, shugaba Kenyatta ya samu kusan kuri’u miliyan bakwai da rabi ko kuma kimamin kashi casa’in da takwas daga cikin dari na dukkan kuri’un da aka kada.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG