Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali Dioncounda Traore ya koma gida, bayan ya shafe fiye da watani biyu a birnin Paris kasar Faransa yana jinyar raunukan daya ji bayan da masu zanga zanga suka nankada mishi dukka a cikin ofishinsa a fadar shugaban kasa.
An dauki tsauraran matakan tsaro sosai a lokacinda Mr Traore ya isa birni Bamaka da maraicen yau Juma’a
Kamfani dilancin labarum Faransa ya bada rahoton cewa shugaban riko kwaryar ya bada sanarwar cewa ya yafe wadanda suka kai masa hari jin kadan bayan ya isa kasar inda Prime Ministan kasar ya tarbe shi.
A watan Mayu masu zanga zanga suka nankada shugaban kashi suka ji masa rauni bayan wata yarjejeniyar siyasa data fadada wa’adin mulkinsa.
Tunda watan Janairu kasar ke fama da rikicin siyasa lokacinda Azbinawa yan aware suka fara borensu.
Shi dai shugaban yana fuskantar rikicin siyasar bayan juyin mulki da kuma karin matsan lambar cewa ya kwace arewacin kasar daga hannun yan yakin sa kai.
Kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS tana so kan ranar tattalin da daya ga wannan wata na Yuli, shugaban ya farfado ko kuma ya yiwa gwamnatin rikon kwaryar kwaswarima ta zama gwamnatin hadin kan kasar.