Shugaban Koriya Ta Kudu ya umurci illahirin jami’an gwamnatinsa su zauna cikin shirin ko-ta-kwana bayan atusaye da bindigogin igwa da aka gudanar ‘yan kilomitoci kadan daga bakin gabar kasar Koriya Ta Arewa. Amma kuma, Koriya Ta Arewa ta janye barazanar maida martani mai tsananin munin da ta yi tun farko, tana mai fada ta bakin kamfanin dillancin labaran kasar cewa wannan atusayen bai kai mizanin da za a maida martani kansa ba. Koriya Ta Kudu ta tura mazauna tsibirin Yeonpyeong cikin wasu dakunan mafaka da aka gina a karkashin kasa, ta kuma tayar da jiragen saman yakinta su na shawagi a samaniya a shirin wannan atusayen awa daya da rabi, inda aka harba igwa har sau dubu daya da dari biyar. ‘Yan jarida dake tare da fararen hula a karkashin kasa sun ce sun ji kasa tana motsi a lokacin harbe-harben. A watan da ya shige, Koriya Ta Arewa ta mayarda martani ga irin wannan atusaye a tsibirin ta hanyar yin luguden wuta, har ta kashe sojoji biyu da fararen hula biyu. Amma a bayan atusayen na yau litinin, hukumomi a birnin Pyongyang sun ce ba zasu maida martani ba a saboda a wannan karon, bindigogin Koriya Ta Kudu sun auna suka yi harbi nesa ne a cikin teku.
Shugaban Koriya Ta Kudu ya umurci illahirin jami’an gwamnatinsa da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana
Shugaban Koriya Ta Kudu ya umurci illahirin jami’an gwamnatinsa da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana