Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce takwaran aikinsa na kasar Venezuela Nicolas Maduro, a shirye yake ya tattauna tare da abokan adawarsa don magance rikicin siyasa a kasar Amurka ta kudun, amma ya gargadi Amurkawa kada su yi tafiya zuwa Venezuela "har sai an bukaci hakan."
Shugaba Trump ya rubuta a shafin sa na tweeter cewa ya na bada shawara ga Maduro da ya tattaunawa da kawo sulhu da 'yan adawa na kasar, da kuma gudanar da zabukan Majalisa. Ya kara da cewa barazanar sanya takunkumin da Amurka ta yi da ya hada da katse hanyar samun kudaden shiga na man fetur na kasar Venezuela sun taimaka wajen sassaucin matsayin Maduro.
A yau laraba ne Maduro ya yi tayin zama a teburin tattaunawar "domin ci gaban Venezuela." A wata hira da kamfanin dillancin labarai na RIA, Amma ya ce ba za’a yi zaben shugaban kasa ba har sai 2025, tare da yin watsi da bukatar da shugaban adawa Juan Guaido, da shugaban jam'iyyar adawa ta Majalisar Dinkin Duniya.
Facebook Forum