Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara inda ake kyautata zaton an aiwatar da harin kunar bakin wake na farko, da ya yi sanadin kashe wani dan sanda ya kuma raunata wadansu mutane bakwai. Bayan zagawa domin ganin irin barnar da aka yi shugaban kasar ya yi kira ga ‘yan Najeriya kada wannan ya razana su, da cewa, ana fama da hare haren ta’addanci a fadin duniya baki daya. Kungiyar addinin Islama mai tsats-tsaurar ra’ayi Boko Haram ta dauki alhakin kai harin da aka kai jiya alhamis kan a bakin shelkwatar yansanda dake Abuja. Fashewar tayi karfi ainun har ta lalata motoci talatin. Hukumomi suna dorawa kungiyar alhakin hare haren da ake kaiwa a arewacin kasar kan jami’an ‘yan sanda da kusoshin gwamnati. Najeriya tayi fama da hare haren bom dake da nasaba da siyasa da kuma kabilanci.
Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara inda ake kyautata zaton an aiwatar da harin kunar bakin wake na farko, da ya yi sanadin kashe wani dan sanda ya kuma raunata wadansu mutane bakwai.