Shugaban kasar Somalia Mohammed Abdullahi Mohamed ya yi alkawarin kara daukar matakan yaki da kungiyar
Al-Shabab, a jawabinsa ga dubban mutane da suka halarci ganganmi a Mogadishu babban birnin kasar domin karrama wadanda harin bom mafi muni da aka kai ya shafa.
Dubun dubatan mutane sun yi jerin gwano a birnin Mogadishu da wadansu manyan biranen kasar Somalia jiya, suna kushewa wadanda suka kai harin da ya kashe kimanin mutane dari uku ya kuma raunata wadansu sama da dari hudu.
Shugaban kasar ya yi kira ga masu jerin gwanon su yi addu’a domin wadanda suka ji rauni a harin da aka kai ranar asabar da gwamnati ta dora alhakin kan kungiyar mayakan al-Shabab.
///SOUNDBITE IN SOMALI///
Mun kebe dala miliyan goma sha hudu na farko, domin yaki da kungiyar al-Shabab, na biyu, domin kafa cibiyoyin kula da marayu. Zamu fara da marayun da suka rasa iyayensu a harin da kungiyar al-shabab ta kai na baya bayan nan.
Kungiyar al-shabab bata dauki alhakin harin ba, da aka kai ranar asabar da ya kasance hari mafi muni da aka taba kaiwa a tarihin kasar Somalia.
Facebook Forum