WASHINGTON, D.C. —
Kwana daya bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kasar Iran a mastayin kasar da tafi hadari a duniya, shi kuwa shugaba Hassan Rouhani, zai gabatar da nashi jawabin gaban taron Majalisar Dinkin Duniya a yau.
Sauran shuwagabanni da suka hada da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da ta Jamani Angela Merkel, sun bukaci Trump da Rouhani, su zauna don tattaunawa bayan taron shekara-shekara, don kawo karshen takaddamar dake tsakanin kasashen biyu.
Amma duk yunkurin bai yi nasara ba.
Suna nan, muna nan, amma bamu cinmma wata matsaya ba, a cewar Trump jiya Talata. Amma Rouhani ya nuna alamun a shirye yake ya gana, amma idan Trump ya yarda ya dage takunkumin tattalin arziki da ya kakabawa kasar.
Facebook Forum