Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka ya zabi shugaban jami'a ya jagoranci babban bankin duniya


Shugaban Amurka Barack Obama da Jim Young Kim
Shugaban Amurka Barack Obama da Jim Young Kim

Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Jim Young Kim wani haifaffen kasar Koriya, domin rike mukamin shugaban babban bankin duniya. Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Jim Young Kim wani haifaffen kasar Koriya, domin rike mukamin shugaban babban bankin duniya. Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Jim Young Kim wani haifaffen kasar Koriya, domin rike mukamin shugaban babban bankin duniya. Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Jim Young Kim wani haifaffen kasar Koriya, domin rike mukamin shugaban babban bankin duniya.

Shugaban Amurka Barack Obama ya zabi Jim Young Kim wani ba-Amurke haifaffen kasar Koriya, wanda a halin yanzu shine shugaban Kwalejin Darmouth domin rike mukamin shugaban babban bankin duniya.

Zaben na Kim, dan shekaru 52 a duniya domin rike mukami mafi girma a cibiyar kudin ta duniya ya zama da ban mamaki. Mr. Obama ya bayyana yau jumma’a cewa, zaben Kim ya rike wannan mukamin ya dace kasancewar Amurka kasa mai mutane daga kowacce fuskar rayuwa, kuma yana da kwarewa kwarai a fannin harkokin kiwon lafiya.

Idan aka tabbatar da zaben nashi, Kim zai maye gurbin Robert Zoellick wanda takardar murabus da ya bayar zata fara aiki a karshen watan Yuni. Ba’amurke ne yake shugabancin babban bankin a kowanne lokaci, sai dai a wannan karon wanda Amurkan ta zata zai fuskanci babbar kalubala.

Kasashe masu tasowa suna so a ba wani daga wata kasa banda Amurka mukamin. Yau Jumma’a kasashen Angola da Najeriya da Afrika ta Kudu suka bayyana goyon bayan ministar harkokin kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala mai kwarewa a fannin tattalin arziki kuma jami’ar diplomasiya a matsayin wadda suke so ta rike mukamin.

Akan zabi shugaban babban bankin daga fannin kasuwanci ko mai kwarewa a fannin banki. Sai dai Mr. Obama ya bayyana cewa, kwarewar da Kim yake da ita a fannin aikin jinya yana da muhimmanci a yaki da talauci da kuma cututuka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG